Dandalin Kannywood: Za'a karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa 7 a kasar Ingila

Dandalin Kannywood: Za'a karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa 7 a kasar Ingila

Labaran da muke samu ba da dadewa a nan na nuni da cewa wasu fitattun jarumai a masana'antar fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywoood da suka tasamma akalla bakwai za su samu kyautar karramawa a kasar Ingila.

Jaruman dai kamar yadda muka samu daga majiyar mu wani babban kamfanin jarida ne na African Voice dake da hedikwatar sa a birnin Landan zai karrama zakakuran jaruman a cikin wata mai kamawa na Nuwamba kuma a ranar hudu ga wata.

Dandalin Kannywood: Za'a karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa 7 a kasar Ingila
Dandalin Kannywood: Za'a karrama fitattun jaruman fina-finan Hausa 7 a kasar Ingila

KU KARANTA: Messi ya ci kwallaye 100 a nahiyar turai

Legit.ng dai ta samu cewa wadanda jaridar zata karrama sune Nafisa Abdullahi (Jarumar da tafi fice); Hafsat Ahmed Idris (Babbar Jaruma); Halima Atete (babbar mataimakiyar Jaruma); Ramadan Booth (Babban jarumi); Sani Ahmad Yaro (Babban mataimakin jarumi); Kamal Alkali (Fitaccen mai bada umurni); Hamisu Lamido Iyantama (Fitaccen mai shirya fina finai).

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai wasu jaruman a masana'atar ta Kannywood sun amshi kyaututtuka da dama a wani buki da aka gabatar a birnin tarayya Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel