Shugaban kamfanin BUA ne na 2 a amshakan matasan masu kudin nahiyar Afrika

Shugaban kamfanin BUA ne na 2 a amshakan matasan masu kudin nahiyar Afrika

Shugaban rukunin kamfanonin nan na BUA mai suna Alhaji Kabiru Rabi'u wanda kuma dan asalin Kano ne ya samu nasarar zamowa na biyu a cikin jerin matasan hamshakan masu kudin nahiyar Afrika masu tasowa.

Shi dai Kabiru Rabi'u ya dai zo na 2 ne a cikin jerin hamshakan masu kudin Nahiyar Afrika su 100 da wata fitacciyar mujalla ta kasar Faransa ta fitar mai suna Institut Choiseul wadda kuma ke wallafe wallafe akan abubuwan da suka shafi nahiyar ta Afrika.

Shugaban kamfanin BUA ne na 2 a amshakan matasan masu kudin nahiyar Afrika
Shugaban kamfanin BUA ne na 2 a amshakan matasan masu kudin nahiyar Afrika

KU KARANTA: Wani babban ma'aikacin gwamnati ya rataye kansa

Legit.ng ta samu dai cewa mai magana da yawun kamfanin mai suna Otega Ogra shine ya sanar da wannan cigaban da shugaban su ya samu inda kuma ya bayyana shugaban nasu a matsayin dan Najeriya daya tilo da ya samu zama a cikin mutane 10 na farko.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa hamshakin mai kudin nan na Nahiyar Afrika Aliko Dangote shi ma dai dan asalin jihar Kano ne kuma shima yana sahun gaba-gaba a jerin masu kudin duniya baki daya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel