Boko Haram ta kai mumunan hari Yola

Boko Haram ta kai mumunan hari Yola

-     Wasu ‘yan kungiyan Boko Haram sun kai wata mumunan hari a kauyen Kuda-Kaya dake Jihar Adamawa

-      An kai harin jiya Alhamis,16 ga watan Yuni

-      ‘Yan ta’addan su kimanin 100 ne suka zo

-      Mutane 10, bayan 18 din da suka rasa rayukan su,sun ji rauni

Boko Haram ta kai mumunan hari Yola
yan Boko Haram

Kakakin jami’an Yan sanda na Jihar Adamawa, Othman Abubakar, ya fada wa Jaridar Xinhua cewa an kai harin jiya da daddare kimanin karfe 10 a garin Yola,babban birnin Jihar. Abubakar ya sake tabbatar da cewa an kama wani dan Boko Haram a garin gombi.

“Har yanzu muna gudanar da bincike domin samun tabbacin cewa wanda aka kama na daga cikin shuwagabannin Boko Haram,” Abubakar ya fada.

Wani mazaunin anguwan, Abdul Ibrahim ya fada da safiyar ranan  jumu’a cewa yan boko haram kimanin 100 suka zo da karfe 10 na dare suna ta harbin kan mai uwa da wabi. Mutane 18 suka mutu a lokacin. Ya kara da cewan,mutane 10 ne suka ji raunuka masu ban tsoro wanda ana sa ran ba za su tsira ba, An kai su asibitin gulak da ke kilomita 3 daga garin.  Yace yawancin wadanda suka rasa rayukan su mata ne da yara.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa wani dan garin mai suna,Jacob Gulak, ya fada wa manema labarai ta hanyar wayar sadarwa cewan ya irga gawawwaki 18 da masu rauni 10. Ya ce la’alla a gano sauran gawawwakin a cikin daji saboda wasu mutanen sun bace kuma ba labarin su.

KU KARANTA: Rundunar Soji sun kai ma ‘Yan Boko Haram wani sabon hari

A wani labarin mai kama da haka, rundunar sojojin Jumhuriyar Nijar sun yi shelar gawawwakin masunta 42 da boko haram ta kashe. An ciro su ne daga cikin rafin chadi da ke kasar kamaru. An baiwa iyalen su gawawwakin domin su birne su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel