Gaskiyar Maganar Gidajen Janar Buratai da ke Dubai

Gaskiyar Maganar Gidajen Janar Buratai da ke Dubai

Gaskiyar Maganar Gidajen Janar Buratai da ke Dubai

– Hukumar CCB tayi magana game da gidajen Janar Buratai na Dubai

– Hukumar ta bayyana cewa tuni Janar Buratai ya bayyana wadannan gidaje cikin kadarorin matar sa.

Hukumar CCB ta Najeriya tayi bayani game da gidajen Shugaban Hafsun sojin Kasar, Janar Buratai da ke Birnin Dubai. Hukumar CCB din tace tuni Janar Buratai ya bayyana wadannan gidaje a cikin mallakar matan sa. Jaridar THE NATION ta fitar da wannan labari.

Gaskiyar Maganar Gidajen Janar Buratai da ke Dubai

Da aka tura sako na FOI domin tabbatar da gaskiyar maganar gidajen na Shugaban Hafsun sojin Kasar, Janar Buratai, shin ko ya saka su cikin abin da ya mallaka, sai aka bada amsa da cewa: “Bayan nadin Tukur Yusuf Buratai a matsayin Shugaban Hafsun soji, ya bayyana duk kadarorin da ya mallaka kamar yadda dokar tsarin mulkin Kasar nan ya nuna.”. Kuma Hukumar ta bayyana cewa, Janar Buratai ya cike takardun CCB-I daga ranar 21 ga watan Yuli inda ya maido ma hukumar a ranar Agusta 21 ga wata na Shekarar 2015. CCB tace: “Muna tabbatar da cewa Gidajen sa na Dubai na cikin abin da ya bayyana a matsayin mallakar mai dakin sa. Mun gode…” Wannan shine abin da shugaban Hukumar ya rubuta.

KU KARANTA: EFCC TA GAYYACI ALI MODU SHERIFF

A ranar 31 ga watan Yulin 2015 ne dai Shugaba Buhari ya nada Janar Buratai a matsayin Shugaban Hafsun Sojojin Kasar Najeriya. Sai dai jaridu sun ta rubutu kan cewa Janar Buratai da kuma matansa 2 sun mallaki wani katafaren gidan a Birnin Dubai na Kasar Larabawa. Tun daga nan, aka tasa hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Kasar EFCC, ta binciki yadda aka yi Janar Buratai ya saye wadannan gidaje guda 2 kan kudi har dala miliyan 1.5. Har ya kai ma wasu na kiran Shugaban Kasar Muhammadu Buhari da ya kori Janar Buratai din.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel