Mata sun yi zanga-zanga a tube a jihar Kaduna

Mata sun yi zanga-zanga a tube a jihar Kaduna

-Mata sun cire tufafinsu a wata zanga-zanga a Jihar Kaduna

-Masu zanga-zangar na zargin cewa Fulani makiyaya na hallaka su da kuma yi musu fyade

-Jami’an tsaro sun ce sun karfafa matakan tsaro a yankin

Mata sun yi zanga-zanga a tube a jihar Kaduna ­
Matan masu zanga-zanga sun fito ne daga yankin Kafanchan ta karamar hukumar Jama'a

Wasu mata sun gudanar da wata zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin su a kan abin da suka ce hare-haren da Fulani makiyaya ke kaiwa a kan kauyukansu.

Matan da sun fito ne daga kauyen Ninte da ke masarautar Godogodo a yankin Kafachan da ke cikin karamar hukumar Jama’a, sun kuma yi zanga-zangar ne a ranar Talata 2 ga watan Agusta shekarar 2016, a fadar basaraken gargajiya na Godogodo kusan a tsirara.

Jaridar The Sun ta ce, wasu mata da suke fama da irin wannan matsala a sauran yankunansu, sun fito  sun marawa matan baya a zanga-zangar, a inda suke zargin cewa Fulani makiyaya sun hallaka mutane a yankin baya da yiwa matan fyade da kone gidajensu da kumka dukiyoyi

Daya daga cikin masu zanga-zangar ta yi zargin cewa, gwamnati ta yi halin ko-oho, da kuma kin daukar matakin da ya dace kan rahotannin da ake kai mata na irin barnar da makiyayan suke yi a kauyukan yankin, a cewar masu zanga-zangar, “gwamanati ta ce mu koma gona, mun amsa kira, amma ta bar mu da makiyaya dauke da makamai su na cin zarafinmu a gonakinmu da gidajenmu”.

A cewar masu zanga-zangar, wasu mazauna kauyukan yanki sun zama ’yan gudun hijira a makwabtan kayukan saboda fargaba.

Malam Iliya Ajiyah, basaraken gargajiya na yankin, ya roki matan su kwantar da hankalinsu , ya kuma kara da cewa gwamnati na kokarin shawo kan lamarin, shi ma shugaban riko na karamar hukumar, Dakta Bege Katukah ya ce an tsaurara matakan tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel