Jihar Sakwato ta fitar da dalibai 39 daga jami’o’in kasar waje

Jihar Sakwato ta fitar da dalibai 39 daga jami’o’in kasar waje

-Gwamnatin jihar Sakwato taba da umurni kan a dawo da wasu dalibai 39 na jihar dake karatu a yanzu a makarantu daban daban a kasar Dubai

-A cewar jihar, a halin da farashin canji ke ciki a yanzu, zai ba gwamnatin damar abije sama da miliyan dari biyar (500) daga cikin manufofin

Jihar Sakwato ta fitar da dalibai 39 daga jami’o’in kasar waje
Gwamnan jihar Skwato, Aminu Tambuwal

Gwamnatin jihar Sakwato taba da umurni kan a dawo da wasu dalibai 39 na jihar dake karatu a yanzu a makarantu daban daban a kasar Dubai.

A halin farashin a yanzu, yunkurin zai ba gwamnati damar ajiye sama da naira miliyan dari biyar (500) daga cikin manufofin. Gwamnatin ta canza ra’ayita na daukar nauyin karatun mutane domin karatu a kasar waje.

 KU KARANTA KUMA: Mai tafiya aikin hajji tayi kashin hodar iblis kunshin 76

Akwai bukatar a dawo da daliban nan ne saboda a rage yawan kudi kuma a mayar da hankali gurin gyara bangaren ilimi,” gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal, ya fadi hakan a ranar Juma’a a Sakwato a lokacin da ya tarbi rahoton kungiyar da aka shirya domin shawartan gwamnatin a kan al’amarin.

Ya kara da cewa an rigada a nema wa dukkan daliban makarantu a Najeriya, yayinda aka riga akayi musu shiri domin tabbatar da cewa babu daya daga cikinsu da ya dawo baya daga matakin da ksuke kai idan sun dawo gida.

Da farko munji cewa, shugaban kungiyar dawo da dalibai, mataimakin gwamna Ahmad Aliyu, yace gwamnati ta yanke shawarar dawo dasu gida sakamakon yawan kudin makaranta a kasar Dubai.

KU KARANTA KUMA: An tabbatar da cutar Lassa a jihohi hudu

Yace gwamnatin ta tabbatar da cewa ta sama masu gurbin karatu jami’o’I kasar da kuma ganin sun koma bakin karatun sub a tare da jinkiri ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel