Tukunya mai tsohon tarihi

Tukunya mai tsohon tarihi

- An gano wata tukunya da mafi girma da kuma yawan shekaru a jihar Kano

- Wasu masu aikin gini ne suka hako tukunyar

- Za a kai tukunyar dakin gwaje-gwaje na kimiyya don  gano yawan shekarunta

Tukunya mai tsohon tarihi

Wasu mutane masu aikin gini a kauyen Rummawa Rangaza a karamar hukumar Ungoggo ta jihar Kano ne suka gano tukunyar.

Ma’aikatan na aikin haka fandishon wani gini ne a kauyen, yayin da suka ci karo da tukunyar a ranar Laraba 21 ga watan Satumba.

Tukunya mai tsohon tarihi

Shugaban Kula da gidan adana kayan tarihi na kasa da ke Gidan Makama a Kano, Mustafa Mohammed Bataka ya yi karin haske game da tukunyar a hirarsa da ‘yan jaridu, yana mai cewa, tukunyar tafi kowacce tukunya da ke hannunsu girma, a gidan adana kayayyakin tarihi, sannan ya kuma ce, da alama tukunyar ta dade, amma ba zai iya kimanta shekarunta ba.

KU KARANTA KUMA: Sabuwa: An gano wata tsohuwar tukunya a jihar Kano

Shugaban wanda ya ziyarci wurin don ganewa idonsa, ya ce, za su zo da kwarraru wadanda za su  haketa, a kuma kai ta dakin gwaje-gwaje na kimiyya a inda za a iya sanin hakikanin shekarunta a duniya.

Ana kyautata zaton cewa manyan tukwane irin wannan mutanen da, na amfani da su ne ko wajen adana ruwa, ko domin tsaro a inda ake jike-jiken magunguna, da siddabaru na tsaron gari.

Mutane da yawa ne ke ta tururuwa zuwa kauyen don ganewa idonsu, an dai taba samun irin wannan tukunya a garin Ririwai da ke karamar hukumar a Doguwa a shekarun 1980, an kuma taba samun kwatankwacinta a unguwar Nomans Land a shekarun 1990 a unguwar Sabongari duk a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel