Labarai
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tafka ta'asa a jihar Akwa Ibom. Miyaguk dauke da makamai sun shiga har cikin coci sun hallaka wanda ya kafa ta tare da babban fasto.
Gidauniyar fitaccen dan kasuwa a Afirka, Aliko Dangote ta sanar da cewa a kullum ta na ciyar da mutane fiye da 10,000 a Kano da kewaye yayin ake azumi.
Babban bankin Najeriya CBN ya kori daraktoci 7, kuma bayanai sun nuna ana shirin sake sallamar wasu ƙarin daraktoci 12 daga aiki, lamarin ya haifar da kace-nace.
Fusatattun dakarun sojoji sun kai farmaki kan maboyar shugaban 'yan ta'addan da ke da hannu a kisan da aka yi wa sojoji 16 a jihar Bayelsa. Sun kona gidaje.
Mahara sun yi ajalin Dagacin Riruwai da ke karamar hukumar Toro a jihar Bauchi bayan sun yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki kafin daga bisani suka hallaka shi.
Wani dan kunar bakin wake ya salwantar da ransa bayan ya tayar da ban din da ke tattare da shi a jihar Borno. Wasu mutum biyu sun jikkata sakamakon tada bam din
Rahotannin sun bayyana cewa wasu sojoji dauke da muggan makamai sun mamaye yankunan gabar tekun jihohin Bayelsa da Delta a ranar Lahadi, 18 ga watan Maris.
Mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwa da ke jihar Sokoto inda ta kone kadarorin miliyoyi wanda har zuwa yanzu ba a tantance asarar da aka yi ba.
Wasu miyagun 'yan ta'adda da ke dauke da makamai sun kai sabon harin ta'addanci cikin dare a jihar Kaduna. 'Yan ta'addan sun yi awon gaba da mutum 87.
Labarai
Samu kari